Wannan shafin mallakarNe 2025-04-11A'ALAMUS-SUNNAH
س : ما أول ما يجب على العباد ؟
Tambaya ta 1:- menene farkon abinda ya wajaba akan bayi (bayin Allah)?
جـ : أول ما يجب على العباد معرفة الأمر الذي خلقهم الله له ، وأخذ عليهم الميثاق به ، وأرسل به رسله إليهم وأنزل به كتبه عليهم ، ولأجله خلقت الدنيا والآخرة والجنة والنار ، وبه حقت الحاقة ووقعت الواقعة ، وفي شأنه تنصب الموازين وتتطاير الصحف ، وفيه تكون الشقاوة والسعادة ، وعلى حسبه تقسم الأنوار ، ومن لم يجعل الله له نورا فما له من نور .
Amsa:- farkon abinda yake zama wajibi akan bayin Allah shine neman sanin abinda Allah ya haliccesu saboda shi. Kuma yariki alkawari tsakaninshi da bayinsa gameda abin, kuma saboda wannan abin Allah ya aiko da manzanninsa zuwa ga bayinsa, hakannan saboda wannan al'amari ne Allah ya aiko da littattafansa zuwa ga bayinsa, kuma saboda wannan abinne Allah ya halicci duniya da lahira, saboda wannan abin Allah ya halicci wuta da aljannah, saboda wannan abin za'a tashi alkiyama, saboda wannan abin mai afkuwa ta afku, saboda wannan abin Allah ya halicci mizani, kuma saboda wannan abin Allah yasa mala'iku suke rubuta littafi (na aiyukan da mutum yake aikatawa a rayuwarsa), sannan wannan abin shiyake jawowa mutum samun dacewa a lahira ko kuma yayi asara ya tabe. Kuma saboda wannan abin Allah yake raba haskensa ga wanda yaga dama. Duk wanda Allah bai sanya masa haske ba toh babu wani haske da zai iya samu.
Idan mukayi duba ga wannan matsashiyar maganar zamu fahimci cewa dukkannin rayuwarmu tana kewaye da wannan abin da malam yafada mana cewa neman saninsa ne yazama farkon abinda ya wajaba akan kowane bawa daga cikin bayin Allah madaukaki.
Sannan a jimlace zamu fahimci cewa neman ilimi shine abinda yazama dole mutum yafarayi kafin ya shagaltu da aiyukan ibada, domin kuwa dama ibada bata yiwuwa sai an hadata da ilimi. Allah yasa mudace.
س : ما هو ذلك الأمر الذي خلق الله الخلق لأجله ؟
Tambaya ta 2:- toh menene wannan abinda Allah ya halicci halittu saboda shi?
جـ : قال الله تعالى : { وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَ }{ مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ } ، وقال تعالى { وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاءَ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا بَاطِلًا ذَلِكَ ظَنُّ الَّذِينَ كَفَرُوا } ، وقال تعالى : { وَخَلَقَ اللَّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ وَلِتُجْزَى كُلُّ نَفْسٍ بِمَا كَسَبَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ } ، وقال تعالى : { وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ } ، الآيات .
Amsa:- Allah yace "bamu halicci sammai da kassai ba domin kawai arikesu ababan/wuraren wasa, bamu haliccesu (sammai da kassai) ba sai don a tsaida addinin gaskiya acikinsu, amma mafi yawan mutane basu sani ba" Allah yace "bamu halicci sammai da kassai haka kawai ba manufa ba, duk dayake dai wannan shine xaton wadanda suka kafirta" Allah yace "Allah ya halicci sammai da kassai ne domin a tsaida addinin gaskiya acikinsu, sannan kuma idan sun mutu an tashesu ayiwa kowane rai sakamako da irin abinda ya aikata a rayuwarsa ta duniya, kuma hakika Allah bazai zalincesu ba wajen yi musu sakamakon" Allah yace "ban halicci mutum da aljan ba sai de don su bauta min ".
Wannan matashiyar maganar tanuna mana abinda Allah ya halicce mu saboda shi, wannan abin shine bauta wa Allah.
Sannan acikin matsashiyar maganar zamuga cewa akwai sakamako bisa duk ibadarda mutum yayi wa ubangijinsa.
Saide wani hanzari ba guduba! Ita bautar Allah ba yadda akaga dama akeyinta ba, ai da Allah yayi nufin mu bauta masa bai kyale mu haka kawai ba, sai da yaturo mana da 'manual' wato littafinda zamu ga yadda yakeso mu bauta masa, sannan bai kyalemu mubi littafin dakanmu ba saida yaturo mana malaminda zai koya mana abinda yake cikin littafin, wannan malamin shine manzon rahama, farin jakada annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam.
Sannan ita ibada idan anyi ta toh tana bukatar wasu abubuwa guda biyu kafin Allah ya amsheta amatsayin cikakkiyar ibada awajensa wadda zai bada lada akanta. Wadannan abubuwan guda biyu sune:-
1-IKHLASI:- wannan yana nufin idan ka tashi yin ibadarka toh ka tabbata kayi domin Allah shi kadai, baka neman yabon mai yabo, baka damuwa da kushen mai kushe, bakason sakamako daga wajen kowa sai Allah shi kadai.
2-MUTABA'AH:- wannan kuma yana nufin idan ka tshi yin ibadar taka toh ba gaban kanka zakayi ba, zaka tsaya ne kaduba yaya annabi yayi wannan bautar kokuma yaya yace ayi kokuma yaya yaga anayi bai hanaba.
Idan muka hada wannan matashiyar maganar da matashiyar magana ta farko zamu samu wani sakamako wanda zai nuna mana cewa ba'a yin bauta sai da ilimi sannan kuma sai anyi ikhlasi da koyi da manzon rahama sallallahu alaihi wasallam.
Sannan zamuga cewa an halicci dan adam ne domin yaxo duniya yayi bautar mahaliccinsa. Ba kamar yadda wasu suke fadaba suke cewa anhalicci duniya da lahira don manzon Allah SAW, tabbas annabi yanada matsayi da darajar da babu wani mahaluki daya taba samunta kuma babu wanda zai sameta anan gaba. Amma maganar cewa domin shi aka haliccci duniya da lahira wannan ba haka bane, domin acikin bayanin da muka kawo abaya zamu ga wata aya da Allah madaukaki yafadi dalilin dayasa ya halicci duniyarsa da lahirarsa, wannan dalilin kuwa shine domin bayinsa suzo su sami wajen da zasu bauta masa(duniya kenan) ita kuma lahira domin ayiwa bayin sakamakon abinda suka aikata a duniyar. Shikuma annabin an halicce shi ne domin yazo duniya yakowa bayi tadda zasu bautawa mahaliccinsu sannan kuma duk wanda yabishi ya tsira wanda kuma ya kaurace masa ya shiga raminda babu shi ba fita har abadan abada.
س : ما هي العبادة ؟
Tambaya ta 3:- mecece ibada(bauta)?
جـ : العبادة هي اسم جامع لكل ما يحبه الله ويرضاه من الأقوال والأعمال الظاهرة والباطنة والبراءة مما ينافي ذلك ويضاده .
Amsa:- ita kalmar ibada(bauta) suna ne wanda yagame duk wani abinda Allah yakeso kuma ya yarda dashi na aiyuka da maganganu na fili dana boye, sannan da barranta daga duk abinda Allah baya so.
Wannan itace bauta, kenan yanzu duk abinda zakayi sai ka auna shi da wannan ma'aunin domin ka samo masa mahalli.
Fadin cewa duk abinda Allah yakeso kuma ya yarda dashi na aiyuka; ana nufin kamarsu sallah, hajji da sauransu, du wanda da jiki ake yinsu.
Fadin cewa duk abinda Allah yakeso kuma ya yarda dashi na maganganu; ana nufin kamarsu karatun qur'ani, hailala, hamdala, takbirai da sauransu.
س : كم شروط العبادة ؟
Tambaya ta 4:- sharadan ibada nawa ne?
جـ : ثلاثة : الأول صدق العزيمة وهو شرط في وجودها ، والثاني إخلاص النية ، والثالث موافقة الشرع الذي أمر الله تعالى أن لا يدان إلا به ، وهما شرطان في قبولها .
Amsa:- sharuddan bauta uku ne.
1-Gaskatawar gabbai
2-tsarkin niyyah
3-dacewa da shari'ah (qur'ani da hadisi) wadanda Allah bai yarda ayi addinisa ba sai ta hanyar koyarwasu
sukuma wadannan guda biyun na karshe sune sharuddan da aikin yake bukata kafin a amshe shi.
Bayanin wadannan abubuwan zai gudana agaba saboda haka ba sai mun fayyace su ba anan.
س : ما هو صدق العزيمة
Tambaya ta 5:- mai ake nufi da gaskatawar gabbai?
جـ : هو ترك التكاسل والتواني وبذل الجهد في أن يصدق قوله بفعله ، قال الله تعالى : { يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لِمَ تَقُولُونَ مَا لَا تَفْعَلُونَ }{ كَبُرَ مَقْتًا عِنْدَ اللَّهِ أَنْ تَقُولُوا مَا لَا تَفْعَلُونَ } .
Amsa:- abinda ake nufi da gaskatawar gabbai shine barin kasala da tawaya wajen bautar, dakuma yin iyaka kokari ta yadda aikin naka zai gaskata furucinka.
Alah yace "yaku wadanda sukayi imani mai yasa kuke fadin abinda baku aikatawa?, ya ishe ku babban laifi awajen Allah indai kuna fadin abinda baku aikatawa".
•fadin cewar aikinka ya gaskata abinda kake fada shine; yadda kake fadin imnai abaki kuma kake fadin musulunci baki bisa so da zabin kanka, toh wajibi ne idann kazo yin ibadar kaji kana yinta ne bisa so ba bisa takurawa ba, ba bisa tilas ba.
ina wadanda idan lokacin sallah yayi suke cewa 'bari muje muyi sallah mu huta/mu sauke nauyi'?
ku tuba ku daina don hakan ba daidai bane.
س : ما معنى إخلاص النية ؟
Tambaya ta 6:- me ake nufi da tsarkin niyyah(ikhlasi)?
جـ : هو أن يكون مراد العبد بجميع أقواله وأعماله الظاهرة والباطنة ابتغاء وجه الله تعالى ، قال الله عز وجل : { وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ } ، وقال تعالى : { وَمَا لِأَحَدٍ عِنْدَهُ مِنْ نِعْمَةٍ تُجْزَى }{ إِلَّا ابْتِغَاءَ وَجْهِ رَبِّهِ الْأَعْلَى } ، وقال تعالى : { إِنَّمَا نُطْعِمُكُمْ لِوَجْهِ اللَّهِ لَا نُرِيدُ مِنْكُمْ جَزَاءً وَلَا شُكُورًا } ، وقال تعالى : { مَنْ كَانَ يُرِيدُ حَرْثَ الْآخِرَةِ نَزِدْ لَهُ فِي حَرْثِهِ
وَمَنْ كَانَ يُرِيدُ حَرْثَ الدُّنْيَا نُؤْتِهِ مِنْهَا وَمَا لَهُ فِي الْآخِرَةِ مِنْ نَصِيبٍ } ، وغيرها من الآيات .
Amsa:- tsarkin niyyah shine bawa ya nufi yardar ubangijinsa bisa dukkanin aiyukansa na magangamu da aiyukansa na fili dana boye.
Allah yace "ba'a umarci(bayi)ba saide domin su bautawa Allah kuma suyi addininsu bisa tsarkin niyya"
Allah yace gameda Abubakar siddiq yayinda yake ciyarda dukiyarsa "baya neman sakamako abindan yakeyi awajen kowa, yanayi ne kawai domin neman yardar ubangijinsa madaukaki"
Allah yafada gameda abinda bayinsa nagari suke fada yayinda suka ciyarda masu karamin hali "lallai mu muna ciyar daku ne kadai don neman yardar Allah, bamuson wani sakamako daga wajenku ko kuma wata godiya"
Allah yace "duk wanda yakeyin aikinsa domin neman sakamako na lahira toh zamu bashi sannan kuma mu kara masa, amma wanda yake aiki domin samun yabo ko lada na duniya toh sai mu bashi a duniyar, amma fa a lahira bashida wani rabo" (akwai ragowar ayoyi da masu yawa dasuke magana akan wannan bangaren )
س : كم مراتب دين الإسلام ؟
Tambaya ta 7:- matakan addinin musulunci guda nawa ne?
جـ : هو ثلاث مراتب : الإسلام والإيمان والإحسان ، وكل واحد منها إذا أطلق شمل الدين كله .
Amsa:- matakan addinin musulunci guda uku ne
1-musulunci
2-imani
3-ihsani
kowannne daga cikin wadannan idan akace za'a fadada shi toh shi kadai ma zai dauki ma'anar addinin.
س : ما معنى الإسلام ؟
Tambaya ta 8:- menene ma'anar musulunci?
جـ : معناه الاستسلام لله بالتوحيد ، والانقياد له بالطاعة ، والخلوص من الشرك ، قال الله تعالى : { وَمَنْ أَحْسَنُ دِينًا مِمَّنْ أَسْلَمَ وَجْهَهُ لِلَّهِ } ، وقال تعالى : { وَمَنْ يُسْلِمْ وَجْهَهُ إِلَى اللَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَى } ، وقال تعالى : { فَإِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ فَلَهُ أَسْلِمُوا وَبَشِّرِ الْمُخْبِتِينَ } .
Amsa:- ma'ana musulunci shine mika wuya ga Allah madaukaki ta hanyarv kadaita shi da bauta, dakuma zurfafawa wajen yi masa makauniyar biyayya, da tsarkaka ga barin hada shi da wani a wajen bauta.
Allah yace "waye yafi kyawun addini fiyeda wanda ya mika wuyansa ga Allah ?"
Allah yace "duk wanda ya mika wuyansa ga Allah kuma yazamanto mai kyautatawa acikin ayyukansa toh hakika yayi riko da igiya mai karfi wadda bata tsinkewa"
Allah yace "kusani cewa ubangijinkiu ubangijine guda daya, ku mika wuya gareshi, sannan yakai ma'aikin Allah kayi bushara(da gidan aljannah) ga wadansa suke kokarin tsarkake niyyoyinsu"
س : ما محل الشهادتين من الدين ؟
Tambaya ta 9:- menene kalmar shahada acikin addini?
جـ : لا يدخل العبد في الدين إلا بهما ، قال الله تعالى : { إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ الَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ } ، وقال النبي صلى الله عليه وسلم : « أمرت أن أقاتل الناس حتى يشهدوا أن لا إله إلا الله وأن محمدا عبده ورسوله » " (1) . الحديث ، وغير ذلك كثير .
Amsa:- bawa baya shiga addinin musulunci sai da ita, domin kuwa Allah madaukaki yace "kadai de muminai sune wadanda sukayi imani da Allah da manzonsa